WASHINGTON, DC —
Dubban 'yan gudun hijira ne a wani sansani dake Maiduguri suka tarbi shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da kuwwar "Sai Buhari" a lokacin da ya kai wata ziyara ta ba-zata a babban birnin na Jihar Borno.
Sai da gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno ya tsawata kafin wannan sowa da 'yan gudun hijirar ke yi ta ragu.
A dai jawabinsa, shugaba Jonathan ya ba 'yan gudun hijirar hakuri, yana mai fadin cewa ya san haloin da suke ciki, kuma nan bada jimawa ba zasu koma gidajensu.
Kafin nan shugaban na Najeriya ya ziyarci barikin sojoji na Maimalari inda yayi jawabi ga sojojin shiyya ta 7 ta rundunar sojan Najeriya, yana mai cewa zai tabbatar da kula da halin rayuwarsu.
Ga cikakken bayani nan daga bakin Haruna Dauda Biu...