ABUJA, FCT, NAJERIYA —
Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta bayarda sanarwar jinkirta babban zaben kasar har sai ranar 28 ga watan Maris na wannan shekarar.
Tun da farko an shirya gudanar da wannan zaben na shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin tarayya a ranar 14 ga watan nan na Fabrairu.
Haka kuma, an mayarda ranar zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohin kasa zuwa ranar 11 ga watan Afrilu, maimakon ranar 28 ga wata nan na Fabrairu da aka shirya tun farko.
Shugaban hukumar INEC, farfess Atahiru Jega, ya bayyana damuwar tsaro a zaman babban dalilin jinkirta zaben. Sai dai kuma mutane da damana ganin cewa wannan wani yunkuri ne na gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan na neman karin lokacin yakin neman zabe ganin yadda iskar siyasar kaar take kadawa a yanzu.