Rahotanni daga Minna a Jihar Neja na fad9in cewa an damke wani jami'in hukumar zabe ta INEC, dauke da takardun kuri'un da aka riga aka dangwala yatsu kan tambarin wata jam'iyya kai a wurinsa, tun ma kafin a bude rumfunan zaben.
Wakilin VOA Hausa, Mustapha Nasiru batsari, yace an kama wannan jami'in zaben ne a karamar hukumar Rijau dauke da wasu kuri'u masu yawa da aka riga aka buga ma jam'iyyar PDP a kai.
Haka kuma a karamar hukumar Magama a jihar ta Neja, an ce shugaban wata jam'iyya ya fita wata rumfa dauke da adduna da wasu makaman tare da wasu matasa inda suka hargitsa shirin zabe. Daga baya an tura sojoji da suka fatattake su, aka ci gaba da aikin jefa kuri'a.
A kasance da www.dandalinvoa.com domin jin bayanai da dumi-duminsu kan wannan zabe na yau asabar.