Nan da makonni biyu sabon agogon Apple Watch zai shiga kasuwanni, agogon da wadanda suka gwada amfani da ita ce na’ura ce mai dauke da fasahar zamanin da watakila babu kamar ta. Amma kuma wannan agogo na Apple Watch ba shi kadai ne agogon na’ura mai kwakwalwa dake kasuwa ba, domin kuwa, babban abokin gasar kamfanin Apple, watau Google, shi ma ya fito da nasa manhajar mai suna Android Wear wadda zata iya sarrafa irin wannan agogo mai kwakwalwa, kuma tuni har kamfanoni irinsu Samsung, LG da Motorola sun fara kera agogo da zasu yi amfani da manhajar ta Android Wear. Kuma wadannan agoguna na Android ba su da tsadar Apple Watch, kuma suna tahowa kala-kala.
Yanzu dai an kaddamar da yaki na wani Agogo mai kwakwalwa ne ya fi? Apple Watch ko mai amfani da Android Wear?
Wajen kawa, agogo mai kwakwalwa na Apple Watch, an kawata shi sosai, kuma abin ado ne da ‘yan zamani zasu so shi matuka. Akwai karami mai fadin milimita 38 ga masu karamin hannu da kuma mai milimita 42 ga masu fadin hannu. Sai dai kuma duk agogon Apple Watch mai kwana hudu ne.
Amma kuma agogo mai kwakwalwa na Android, yana zuwa ta kowace irin siffa mutum yake so, ko mai kwana hudu ko round. Daga cikin wadanda ke kasuwa, Motorola Moto 360 da kuma Huawei Watch sune masu kyau ga ido. Sauran dai sun fi kama da irin agogo nay au da kullum da aka saba gani.
Akwai kuma bambance-bambancen yadda Apple Watch da Android Wear suke nunawa mutum App.