Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fasahar Gano Mutum Ta Hanyar Karanta Kwayar Idonsa Daga Nesa


Cibiyar Binciken Halittar Dan Adam ta Jami’ar Carnegie Melon a nan Amurka ta bullo da wata sabuwar fasahar da zata iya gane mutum daga nisabn kafa 40 ta hanyar karanta kwayar idonsa kawai.

A cikin wani faifan bidiyo dake nuna wannan sabuwar fasaha, darektan cibiyar, marios Savvides, ya shiga cikin mota yana zaune yayin da wasu abokan aikinsa suka iya gano shi ta hanyar auna kamara jikin madubin motar, inda tana ganin kwayar idonsa ta iya gano shi.

Kwmafutar dake jikin kamarar ta iya auna bayanin kwayar idonsa da ta gani da wanda ke cikin na’ura, ta kuma nuna sunansa da sauran bayanansa.

Jami’ar Carnegie Melon ta ce wannan fasahar tana iya aiki daga nisan mita 12 ko kafa 40. Haka kuma, ba kamar irin fasahar da ake amfani da ita wajen karanta kwayar ido a yanzu ba, wannan tana bukatar kamar kwaya daya tak ce maras tsada.

Hukumomin tsaro zasu iya cin moriyar wannan fasaha wajen gano ‘yan ta’adda ko mutanen da ake nema ko da sun buya a cikin taron jama’a ne.

XS
SM
MD
LG