Kasuwanci ba wai don cin riba akeyinshi kawai ba, wata hanyace ta tallafawa masu karamin karfi, harma da msu hannu da shuni. Malama Sha’awa Sabuwar Gandu, mace mai kamar maza, batayi kasa a gwiwa ba, wajen ganin ta taimakama kanta da ma al’umar ta wajen samun kudin shiga, ta kasance tana sana'ar saida kayan gwanjo da gumama, don kuwa wadannan kayan na masu karamin karfi ne.
Babban abun jin dadinta da wannan sana’ar tata shi ne, yadda take bama mutane kaya koda ko bashine suna mata godiya, don wasu lokutta da dama takan sayar da wasu kayan cikin faduwa, amma masu saye na jin dadi itama tana murna, wannan shine yake kara mata karfin gwiwa wajen jajircewa ta yi wannan sana’ar.
A bangare daya kuma, tana ganin wannan wani lokaci ne da yakamata ace kowace mace ta tashi tsaye, wajen ganin ta yimakanta abunda ballalai sai maigida yayi mataba, musamman ma akan ‘yayanta. Don yanzu zamani ya chanza, kuma mata sukasance masu nuni ga ‘yan’uwansu mata su tashi tsaye wajen neman sana’ar da zasuyi tunkaho da ita a gaba. Su sanifa, sune iyayen kasa, ashe kuwa yaransu zasu yi kokarin koyi dasu don haka yazama wajibi ga iyaye mata su mike tsaye wajen neman sana’a, da zasu bada ta dasu gudunmawa wajen ciyar da kasa gaba.