Daruruwan matasa ne sukayi wata zanga-zanga lumana a cikin kwaryar jihar Kano, mafi akasarin wadannan matasa masu nasana’ar sufurine na a Dai-daitasahu, sun yi korafi dacewar gwamnati na kokarin hanasu cin abinci, domin kuwa sun bayyyanar da cewar kudin haraji da aka samusu domin sabunta rajistasu ta a Daidaita sahunsu yayi yawa.
A tabakin wasu daga cikinsu, sun bayyanar da cewar an umurcesu dasu biya kimanin naira dubu goma sha bakwai, bayaga kudaden haraji da suke biya a kowace safiya, suna ganin wanna yazama da akwai wahalaswa. Don haka suke kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta dubi Allah ta tausaya ma matasannan, domin kuwa wannan tsananin kan iyasa wasu da dama cikin halin kakanikanyi.
A tabakin shugaban hukumar Karota Alhaji. Mustapha Hamza Buhari, yayi karin haske dangane da korafin wadannan matasan dacewar, harajin da akasamusu ba wadannan makudan kudin da suka anbato bane, abun da aka bukacesu dasu biya shine naira dubu biyu. Donmin kuwa wadannan kudaden dasune ake amfni wajen gyaran hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa. A bisa dalilin haka yayi kira ga matasannan dasu kokarta biya wadannan kudin don gujema fushin hukuma.