Hukumar horas da ma’aikatan gwamnati, da mana kamfanoni masu zaman kasu ta kasa. Tare da horas da matasa ga wasu sana’o’in hannu a Najeriya, wacce ake kira “Industrial Trust Fund” a turance. Ta dau alwashin horas da kimanin matasa Milliyan biyu a cikin kowace shekara. Wadannan matasan zasu samu haraswa a kowadanne bangarori na yau da kullun, wadan da suka hada da aikin kafinta, kira, walda, dinki, jima, da dai makamanta hakan. Wannan tsarin yazo ne a lokacin da ake da bukatar hakan a cikin kasar, kasancewar rashin aikin yi, yayi yawa musamman ma ga matasa.
A wata tattaunawa da DandalinVOA yayi da Malam Sale Garba Katsina, shugaban hukumar reshen birnin tarayya Abuja. Yayi muna karin haske dangane da irin shirye shiryen da hukumar tasu take yi, don ganin ta wadatar da matasa da ilmumuka na kowace irin sana’ar hannu, da kuma yadda zasu yi kokarin dogaro da kansu. Hukumar tasu tana da ressa a kowa ce jiha da Abuja, duk matasahi wanda bai da aikin yi, to ya garzaya wadanna ofisoshi nasu, a kowace jiha don samu yaci gajiyar wanna shirin.
A yanzu haka suna kokarin ganin sun hada gwiwa da hukumar masu yima kasa hidima, don ganin matasa da suka kamala karatun su na jami’a sun samu horaswa da zasu iya dogaro da kan su batare da sai sun yi aiki ba. Ya kara da cewar horon da suke bama matasa a kowane fanni, suna da hadin gwiwa da kasar Singafo da Brazil, duk don ganin sun bada horaswa mai nagarta, ba don komai ba sai don duk inda suka bama mutun takardar sheda, yaza mana zai iya aiki a ko ina a duniya.