Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gayu Da Tabin Hankali Sai Zuwa Lahira


Mutuwa dole
Mutuwa dole

A tabakin wasu masana, wanna sabuwar sana’ar da matasa suka sa kansu ciki na da wani suna “Tabin Hankalin Zamani” wanda ake cema "Selfie" a turance. Wanna ba wani abu bane illa yadda matasa maza da ‘yan-mata suke da wata dabi’a, na daukan kan su hotuna da wayar hannu, a kowane irin yanayi suka samu kan su ciki. A lokkuta da dama matasannan kan dauki kawunan su hotuna don sasu a shafufukan su na yanar gizo, wani lokaci don burge abokan su.

Domin kara tabbatar da wanna suna na wanna haukar zamanin, ranar Talata wani matashi dan shekaru goma sha tara 19, ya kashe kanshi a yayin da yake daukan kanshi hoto a lokaci yada. Wanna matashin dai ya dauki bindiga, yasa a kanshi hannu daya kuma na rike da wayar zamani don daukan hoto, wanda cikin wanna yana yi da yake, ya kashe kanshi har lahira.

Wanna matashin dai na da ‘yaya biyu, har zuwa wanna lokacin ba’a bayyanar da sunan wanna matashin ba, kuma jami’an ‘yan-sanda na garin Houston a jihar Texas, na cigaba da binciken yadda wanna abun yafaru. Duk dai da cewar iyayen shi sun musanta abkuwar wanna abun.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG