Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaruman Bollywood Da Suka Doke Na Amurka Wajen Samun Kudi


Mafi yawan mutane a Amurka ba su taba jin sunan Amitabh Bachchan ko Salman Khan ko kuma Akshay Kumar ba, amma kuma wadannan jaruman fina-finan Indiya ko Bollywood, sun samu kudin da ya zarce na fitattun jaruman Amurka irinsu Mark Wahlberg, Dwayne Johnson da Johnny Depp.

A karon farko, da aka zo auna jaruman da suka fi samun kudi cikin wannan shekara a fadin duniya, ba wai kawai jaruman Amurka da aka saba gani aka duba ba. An auna jarumai daga kowace kusurwa domin tabbatar da cewa lallai wannan jerin na duniya ne a zahiri.

Mujallar Forbes da ta yi wannan aikin, ta ce jarumai 12 suka shiga cikin wannan jerin a karon farko, biyar daga cikinsu daga kasar Indiya. A bayan Amurka, kasar Indiya ce ke da jarumai mafiya yawa a cikin jarumai 34 dake wannan jerin.

Wadannan jaruman na Indiya su biyar, abinda suka samu a shekarar nan ya kai dala miliyan 140 da rabi. Watau Naira Biliyan 28 har da wasu miliyan 100 a kai!

Daga cikin wadannan jarumai na Indiya ko Bollywood, akwai guda 3 wadanda sun a ma cikin jarumai 10 da suka fi samun kudi cikin wannan shekara a duk fadin duniya.

Amitabh Bachchan da Salman Khan, kowannensu ya samu dala miliyan 33 da rabi, watau Naira Biliyan 6 da wasu canjin Naira miliyan 700 a kai, kowannensu ya samu a shekarar nan. Abinda Amitabh Bachchan kawai ya samu ya zarce abinda shahararrun jaruman Amurka Chris Pratt da Ben Afleck suka samu idan an hada su wuri guda ma.

Amitabh, mai shekaru 72 da haihuwa, ya cika aljihunsa sosai daga wani fim mai suna Bhoothnath Returns da yayi a 2014, ga kuma abinda yake samu daga wani shirin talabijin na kacici-kacici da yake gabatarwa mai suna Kaun Banega Crorepati, Ina mai son zamowa miloniya?

Shi kuma Salman Khan, yayi kunnen doki wajen samu da Amitabh Bachchan duk da kaurin sunan da yayi. A watan Mayu na wannan shekara ta 2015, an yanke ma Salman Khan hukumcin daurin shekaru 5 a kurkuku a saboda buge wani mabaraci da yayi har lahira da mota a 2002. Yanzu an bar shi yana zaman belo yayin da yake daukaka karar wannan hukumcin.

Shi ma Salman Khan yayi fim mai suna Kick wanda yayi farin jinni a 2014, yana kuma da masoya masu dan Karen yawa. Akwia shirinsa na talabijin mai suna Bigg Boss da yake gabatarwa.

Akshay Kum ar shine na 9 a duk duniya da dala miliyan 32 da rabi, watau Naira Biliyan 6 da wasu ‘yan canji na Naira miliyan 500 a kai. Abinda Akshay ya samu ya kai na a hada George Clooney da Brad Pitt wuri guda. Shi ma yayi fim mai suna Holiday da kuma wani mai suna Entertainment a 2014, sannan yana gabatar da wani shirin talabijin mai suna Dare 2 Dance.

Shah Rukh Khan shine na 18 a duk duniya, kuma na 4 a cikin jerin jaruman Indiya. Abinda ya samu shine dala miliyan 26, ko Naira Biliyan 5 har da miliyan 200 a kai. Ya samu sosai a wasu fina-finan da suka hada da Happy New Year da Fan, sai kuma tallar da yake yi ma kamfanoni kamar Pan Masala.

Na biyar a cikin jaruman Indiya da suka fi samu a shekara guda da ta shige shine Ranbir Kapoor, wanda ya samu dala miliyan 15, ko kuma Naira Biliyan 3. Duk da cewa abinda ya samu bai kamo kafar na su Amitabch ko Salman ko Akshay ko kuma Shah Rukh Khan ba, Ranbir Kapoor ya doke jarumawan Amurka fitattu irinsu Chris Pratt da Chris Evans da kuma Andy Lau daga Hong Kong.

Mutane da dama suna tambayar ko ta yaya jaruman Bollywood suke samun irin wannan kudi mai yawa haka? Amsar ita ce duk da cewa fina-finan Indiya basu samun kudi kamar na Amurka a gidajen sinima, suna sayarda iznin nuna fina-finansu ga gidajen talabijin na tauraron dan Adam ko satalite. Sannan kuma a duk lokacin da aka nuna fim na Indiya, to Jaruman suna da kaso na kudin da aka samu da ake basu.

XS
SM
MD
LG