Masu iya magana kan ce “Kowa ya bar gida, gida ya barshi” Sau da dama akan samu wasu mutane, musamman mutane da suka fito daga kasa she masu tasowa, kamar kasashen dake nahiyar Afrika, Asiya, kudancin Amurka, su kan zabi wasu kasa she da suka cigaba fiye da nasu kasa shen haihuwa ko asali.
Wani shahararen dan fim mai suna Robert Pattinson, a nan kasar Amurka amma dan asalin kasar Ingila ne, ya bayyanar da cewar babu zagin da za’ayi mishi mai ciwo irin a kalle shi ace mishi, shi Ba’amerike ne. Yace wanna shine abu mafi muni gare shi da zuri’arshi.
Don haka yanaso mutane su sani, shi bai yada gidan su ba, kuma don kasar Amurka tana kasa mai arziki, bai zama wani dalili da zai sa yabar tushen shi ba. Duk dai da cewar yanzu yana zama tsakanin garin Los Angeles a jihar Nivada a nan Amurka, da Ingila, kuma yana sha’awar kasashen yankin turai baki daya.
Ya bayayanar da cewar tun a shekarar 2008 da waya da kafofin yanar gizo sukayi karfi, yake tasamun karin masoya a duniya. Wannan yasa mishi karin farin jinni. Don haka kada mutun yaki dangin shi da asalin shi, koda kuwa yasamu kanshi a wani hali.