Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsun-Tsaye Ba Don Ci Kawai Allah Ya Halicce Su ba


Tsun-tsu mai wayo
Tsun-tsu mai wayo

Wani bincike da aka gudanar a jihar Arizona ta nan kasar Amurka, na nuni da cewar, za’a iya amfani da wani tsun-tsu wajen zama mai gadi a gida. Domin kuwa wannan tsun-tsun, yakan yi kwai kuma ya zauna akan kwan na shi na tsawon lokaci mai yawa a rana. Shi dai wannan tsun-tsun mai suna Tiny, bai cika yawo ba.

Masu wannan binciken sun gano cewar wannan tsun-tsun idan aka ajiye shi a mashigin gida wanda idan duk wani bako da ba dan gida ba, yazo wannan tsun-tsun zai yi kuka. Wanda ba zai dena kuka ba har sai masu gidan ko fuska sani tazo a gare shi.

A wannan binciken na su, sun gano cewar ba kawai Aku ne tsun-tsu mai hankali ba, akwai tsun-tsaye da dama masu hankali, wadanda idan mutane za su dinga koya musu abubuwa, zasu koya kuma su aiwatar a kowa ne lokaci ake bukatar suyi. Don haka suna kara kira ga al’uma da suyi amfani da damar da Allah, ya basu, da arzikin dabbobi, ba kawai su zama abun ci ba, batare da anyi wani amfani da su ta yadda yakamata ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG