A wani bincike da wani farfesan binciken laifufuka, shari’a da adalci. David Maimon, na Jami’ar Maryland da ke kasar Amurka, ya gudanar ya yi nuni da cewar, akwai abubuwa da dama da yakamata mutane masu mu’amala da shafufukan yanar gizo su guje ma.
Abu mai sauki ne muta ne su saba da aikawa da sakonni ta yanar gizo, ko masu amfani da shafin zumunta na facebook, twitter, Instagram, da dai makamantan su. Wajen raba labarai, ko bayanai da wadanda basu san asalin su ba. Kawai mutane kanyi hakan da zarar sunga wani labari, yayi musu dadi sai kawai suyi ta aikawa da shi ga wasu.
Ko kuma mutane kanje wasu guraren jama'a, da ake bada yanar gizo kyauta sai kawai su dinga hada na’urorin su da wannan kafar yanar gizon, sau da dama mutane kan sace baya nai a wayoyin mutane, a wannan lokacin da aka hada waya don samun yanar gizo.
A wasu lokkuta ma akan samu damar satan bayanan mutun na murya, kana da lambobin sirri na mutun. Don haka akwai bukatar muta ne su guji bude wayoyin su a wajajen da basu da tabbacin sirri, da kuma karfin gwiwar baza’a yi musu wani lahani ba.