A shekarar 1983, kimanin shekaru talatin da biyu 32, da suka wuce, a karon farko da aka taba samun mace bakar fata, ta zama sarauniyar kyau din kasar Amurka.
Vanessa Williams, ta samu damar zama mace ta farko da ta fito daga jinsin bakar fata, da aka zaba a matsayin mace da tafi kowa kyau a kasar Amurka. Bayan bata wannan matsayi, sai aka umurce ta don dole ta ajiye wannan matsayin.
Dalili kuwa shi ne, an ga hotunan ta a wata jarida, da suka nuna tsirai cin jikin ta, don kuwa a wannan lokacin hakan ya saba ma al’adun kasar. Ita dai mawakiyar Vanessa, a karon farko tasamu takarda a hukuman ce, da ke bata hakuri dangane da matakin sata barin matsayin ta na mace mafi kyau a shekarun baya.
A tabakin shugaban hukumar tan-tan ce mata da su kafi kyau ta Amurka, Mr. Sam Haskell, “Ina so nayi amfani da wannan damar, don na baki hakuri a madadin hukumar mu, na abubuwan da aka ce a kan ki, da kuma akayi miki wanda yasa baki ji dadi ba”