Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Mata Na Ganin Samari Tsamaye Ne A Wajen Shan Codeine


Kwayoyi
Kwayoyi

Shaye-shaye yazama ruwan dare, ba kawai a tsakanin samari ba, harma da ‘yan-mata. Wani bincike da aka gudanar a jihohin Arewacin Najeriya, na nuni da cewar dubban ‘yan-mata da matan aure, ke shan maganin tari da ake sha don maye.

A zantawa da mukayi da wata, ta bayyana muna cewar ai a wannan zamanin, idan ba mace na shan irin wadannan abubuwan ba, to kawayen ta ma suna ganin ta kamar bata waye ba. Kuma su matan aure ai sai sun sha wannan maganin kafin su iya zama da mazajen su lafiya, domin kuwa idan suka sha magani sai suji dai-dai, kuma baza su iya fada ba. Don haka shan maganin na kawo zaman lafiya, tsakanin matan aure da mazajen su, mu kuma ‘yan mata da samarin mu da ma iyaye da mutanen anguwa.

Mun duba illar wannan shaye-shayen, musamman ma ga mata da matasa, shan wannan maganin dake dauke da wasu sunadarai, na kashe garkuwar jiki, yana lalata hanta, kana yana lalata kwa-kwalwa ta matasa, tun da kuruciyar su. Don haka duk inda aka ga masu wadannan shaye-shayen, to lallai hakin kowa ne a sanar da hukumomi, don daukar matakai da suka kamata, domin rashin yin hakan zai haifar da masifu da dama a cikin al’uma.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG