Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Majalisar 'Dinkin Duniya Na Shekarar 2015


Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

A ranar Juma’a da ta gabata ne Majalisar Dinkin Duniya, dake zama a jihar New York ta kasar Amurka, suka fara taron kwanki bakwai 7, na shekara-shekara don duba matsalolin da kasashen duniya ke fuskanta da kuma hanyoyin da za’abi don magance su. A wannan shekarar an maida hankali ne akan matsaloli da suka hada da Talauci, Yunwa, da habbakawa da gyaran yanayin kasashe nan da shekaru goma sha biyar 15.

Muradun karnin na gomasha bakwan 17 da aka sa a gaba, wadanda aka tattauna akan su na tsawon shekaru uku 3, a tsakanin kasashen dari da casa'in da uku 193, da suke cikin kungiyar ta Majalisar Dinkin Duniya. Duk za'a duba su ne don gano hanyoyin da suka kamata a bi, don gyara a tsarukan gwamnatocin kasashe a nan gaba.

An kuma sa abubuwa goma sha bakwai 17, a gaba don ganin anyi maganin su a wadannan kasashe dari da sittin da tara 169, da suka hada da zaman takewa, tattalin arziki, da sauran matsaloli da suka shafin girgizar kasa. Yanzu dai za’a maida hankali ne don ganin anyi nasara wajen wadannan abubuwan daga farkon shekara mai zuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG