Hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya, dake aiki a Najeriya, sun bayyanar da irin nasarar da aka samu a Najeriya, wajen yaki da cutar shan-inna. Sun ce wannan wani babban nasara ne a wajen yaki da wannan annobar, mai nakasar da yara. Domin kuwa nasara a Najeriya, na nuni dacewar ana iya magance ta a duniya baki daya.
Anyi nasarar magance cutar a Najeriya, amma har yanzu cutar na da saura a kasashen Pakisatan da Afghanisatan. A gaskiya kauda cutar a wadannan kasashen biyu jan aiki ne, hakan yasa suka kara shekara daya daga yadda aka tsaro a baya, don magance cutar a duniya baki daya, zuwa shekara 2019.
Akwai kuma bukatar samun karin kudi da suka kai kimanin dallar Amurka, Billiyan daya da rabi $1.5 B. don magance sauran cutar a duniya baki daya. Shekaru uku da suka wuce itama kasar Najeriya, tana cikin kasashe da suka fuskanci matsalolin cutar, amma yanzu anyi nasara. Sai dai akwai bukatar mutane su maida hankali, wajen tsaftace muhallai don gujewa dawowar cutar, da ma wasu cututtuka da kan iya barazana ga lafiya mutane.