A yau mun tattau na da wani dalibi mai karatun digirin digir-gir, mai suna Abubakar Idris, ya kuma fara da gabatar da kanshi kamar haka. An haifeni ne shekaru talatin da biyu da suka wuce, a unguwar da ake kira Gyallesu na karamar hukumar Zaria a cikin jihar Kaduna.
Yaci gaba da cewa, na fara neman ilimin zamani ne daga firamaren Gyallesu in da na samu takardar shaidar kammalla firamaren. Bayan nan, sai na tafi makarantar Sakandaren gwamnati da aka fi sani da Chindit Barracks in da na samu shaidar kammalla karatun sakandare da ake kira SSCE. Da ganan, sai na wuce makarantar horas da mallamai dake Zaria (FCE Zaria) in da na samu shaidar NCE. Sa’annan, na cigaba da karatun digiri na farko a babban Jami’ar Ahmadu Bello University (ABU) dake Zaria. Bayan karatun digiri na farko, nayi aikin bautawa kasa (NYSC) na tsawon shekara daya a makarantar sekandaren gwamnatin tarayya (FGC) dake garin Ikot-Ekpene dake jihar Akwa-Ibom na kudancin Najeriya.
A shekarar dubu biyu da goma ne dai, na samu Fulbright scholarship domin zuwa kasar Amurka karantar da harshen Hausa ga turawa a Jami’ar jihar Michigan na tsawon shekara daya. Na karantar da dalibai Amurkawa dake shawa’ar koyon harshen Hausa da kuma al’adun Hausawa ne tare da taimakon sashen dake nazarin nahiyar Afirka ne, wato African Studies Center. Shi wannan Fulbright scholarship kuwa ana gudunar da shi ne a kowace shekara ta ofishin jakadanci Amurka dake Abuja.
Bayan na kammalla wannan aikin sai na samu admission na yin karatun digiri na biyu wato Masters a bangaren tafiyar da tsarin ilimi da makarantun firamare da kuma sakandare a wannan jami’a ta jihar Michigan wadda aka fi sani da Michigan State University. Ko da na samu wannan admission na karo karatun Masters ba ni da wani scholarship da zai taimaka min na biya makurdan kudi domin wannan karatun, na biya dalar Amurka dubu talatin zuwa talatin da biyar wato naira miliyan biyar da rabi zuwa shida dai-dai. Ko da na koma gida Najeriya, na yi shirin dawowa na fara karatun, amma ni da iyaye na bamu da karfin sayen tikitin jirgin da zan dawo Amurka. Da taimakon Allah da abokan aziki na samu kudin tikitin jirgi amma babu kudin makarantar da zan biya.
A cikin watan disamba na shekarar dubu biyu da shabiyu ne na kamo hanyar dawowa Amurka daga babban filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammed da ke Legas. Ko da na isa Jami’ar jihar Michigan sai na kama aikin a gidan abincin dalibai na awa-awa domin na biya kudin makaranta da kuma da kuma wajen kwana. Da wannan kudin aikin gidan abincin dalibai ne na biya kudin makaranta na tare da gidan da na zauna har sai da kammalla wannnan karatun digiri na biyu a shekarar dubu biyu da sha hudu dai-dai.
Da kammalla wannan karatun nawa na Masters, sai Jami’ar ta bani admission din karatun digirin digirgir wato wanda ake kira Ph.D. kenan a turance tare da scholarship da nake aiki a mastayi na matakin darakata na gidan kwanan dalibai wanda yake biyan mun kudin makaranta, daki, da kuma dan alawus din kudin kashewa. Yanzu haka dai ina cikin shekara na biyu kenan na wannan matakin karatun kuma ina fatar gamawa ne shekara biyu masu zuwa in Allah ya yarda.
Matasa da suka kammala karaun sakandire kuma suke da sakamako mai kyau suna iya zuwa daya daga cikin wannan shafin don su samu gurbin tallafi na karatun jami'a a kasashen duniya kyauta. http://mcfscholars.isp.msu.