Dan-sanda abokin kowa! Wata yarinya mai suna Serynity Rickett, ‘yar shekaru takwas 8, ta kira layin taimakon gaggawa mai lambar 911, domin sanar da hukumomi dangane da sabuwar keken da aka sace.
A lokacin da ta kira lambar, dan-sanda Matt Jarrett, shi ya dauki wayar, yarinyar ta gaya mishi cewar, an sace mata keken ta da iyayen ta suka siyamata a lokacin da ta cika shekaru takwas 8. A cewar dan-sandan a lokacin da ya isa gidan iyayen yarinyar, ya tarar da baban yarinyar cikin wani hali na damuwa, domin kuwa iyayen sun yi asusu don su siyawa 'yar su keke, a lokacin bukin zagayowar haihuwar ta, amma wani mara gaskiayar ya sace keken.
Yarinyar ta gaya ma dan-sanda cewar, tana da masaniyar cewar iyayen ta sunyi kokari wajen tara kudi, don siya mata wannan keken, amma kawai rana tsaka wani ya sace. Dan-sandan dai ya nuna rashin jin dadin shi, a lokacin da yaga baban yarinyar na kuka yana cewar, basu da kudin da zasu sake sayamata wata sabuwar keken. Dan-sandan ya dau alkawalin saya mata wata sabuwar keke.
A lokacin da dan-sandan ya iso gidan su yarinyar da sabuwar keke, iyayen ta sun nuna jin dadin su, itama yarinyar ta ji dadi matuka. Dan-sandan ya roki jama'a da su guji daukar kayan da ba nasu ba.