Kamar lokacin hutu na karshen shekara ya zo wa sashen sarrafa basira da jimla na kamfanin Google da wuri. Kamfanin Google da hukumar NASA da kungiyar hadakar jami’o’i ta binciken sararin samaniya, sun sanar cewa zasu sayi computer 2x ta kamfanin D-Wave, wadda ita ce mafi sabunta, kuma mafi inganci da karfi cikin ire iren computer masu sarrafa aiki da adadin jimla da ake samu yanzu a kasuwa.
Computer mai suna 2x ta ninka adadin ‘ya’yan jimlar sarrafa aiki da computer kamfanin D-Wave ta da ke da ita a da, zuwa ‘ya’yan jimla (quibits) 1000, kuma tana aiki ne akan adadin ninki ba ninkin sanyi (millikelvin) 15, wanda yake da tsananin sanyi. A yarjejeniyar da suka yi ta shekara bakwai, kamfanin D-Wave zai bawa Google duk wata sabuwar computer mai kamar wannan da zasu kirkira nan gaba.
Sabuwar computer zata ci gaba da aikin dake gudana yanzu a dakin kirkire kirkire na Google na ingancin sarrafa matsaloli da koyon aiki da inji, inda kungiyoyin kawancen zasu raba lokaci na aiki da computer.