A shirin namu na yau, mun duba yadda ake gudanar da karatun sakandire, a kasar Amurka ne da kuma irin banbance-banbance da suke da shi da makarantu a Najeriya.
Abdulsalam Nasiru Dan-Mowa, mai shekaru goma sha shida 16, dalibi a makarantar sakandire aji biyar 5, “SSS 2” a jihar Florida, ta nan Amurka. Ya fara da gabatar da kan shi da kuma yi muna karin bayani dangane da irin canji da yagani a makarantar su ta nan Amurka da ta Najieriya.
Abu na farko da ya nuna shine, malamai a nan Amurka, sukan bama dalibi lokaci da yakamata ace dalibi ya samu daga malami, don fahimtar karatu, dangantaka mai kyau a tsakanin su da malaman su itace tasa suke fahimtar karatu sosai. Dalibai na samun damar zaban irin abincin da suke so suci a kowace rana, wanda gwamnati ke daukar nauyin hakan.
A tsarin makarantun su, akwai damar da dalibai kan samu, na nuna hazaka wanda a karshen sati akan saka hoton dalibin da yafi kokari a satin, a gaban makaranta, haka shima dalibin da yafi kokari a watan za’a saka hoton shi don kowa ya gani. Hakan dai yanasa kowane dalibi yayi kokari don a saka hoton shi, wannan wata hanya ce da ake bama dalibai kwarin gwiwa wajen karatu.
Abdulsalam, yakara jawo hankalin ‘yan-uwanshi matasa, da su maida hankali wajen neman ilimi, don yin dai-dai da zamani, wanda ilimi shine hanyar da duk wani matashi ya kamata ace yabi don cimma burin rayuwa.