Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matukin Jirgin Sama Ya Mutu A Sararin Samaniya


Flight Control Delays
Flight Control Delays

Matukin jirgin saman kamfanin jiragen sama na “American Airlines” ya mutu bayan tashin jirgin. Jirgin dai ya tashi dauke da fasinjoji dari da arba’in da bakwai (147). Sun tashi a tsakanin garin Phoenix da Boston.

Shi dai matukin jirgin, Captain Michael Johnston, mai shekaru hamsin da bakwai (57), yana tuke da jirgin sai ya ji jikinshi baya ma shi dadi. Mataimakin matukin jirgin, ya dauki ragamar jagorancin jirgin, kuma ya samu nasarar saukar da jirgin kasa lafiya.

Sauran ma’aikatan jirgin, sun yi kokari wajen kwantar ma fasinjojin da hankali, wanda ba a sanar da su cewar, matukin jirgin ya rasu ba, har sai bayan saukarsu. A cewar shugaban kamfanin, yace babu abun da yafi dadi irin aiki da mutunta abokan aiki, wanda hakan ya sa babu wata matsala tsakanin ainihin matukin da mataimakin shi. Domin kuwa duk inda aka ce ana aiki babu fahimta, to za a iya samun matsala, wajen ba ma kowa taimako idan hakan ya bukatu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG