Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tangardar Fasaha Ta Haddasa Rudani Ga Jama'a


Jirgi
Jirgi

Wata ‘yar tangarda da aka samu a fasahar jiragen kamfanin “Southwest Airlines” ta haddasa jinkiri ga daruruwan mutane da suke shirye-shiryen tafiye-tafiye ta kamfanin. A jiya Lahadi ne daruruwan mutane basu samu damar barin tashoshin jirgin kan kari ba, domin kuwa ma’aikatan kamfanin sun koma duba takar dun mutane da hannu, batare da amfani da na’ura mai kwakwalwa ba.

Ma’aikatan kamfanin su kace "Muna fuskantar wasu matsaloli da suka shafi fasaha al'amurran da suka samii, shafin sun a yanar gizo na Southwest.com, kana da kuma wajen ajiyar wurare na cibiyoyin da filayen jiragen saman su ke sauka, na fuskanatar wasu ‘yan damuwa. Kamfanin jirgin sama ya ce a cikin wata sanarwa. Da kamfanin jirgin sama ya tabbatar da cewar wasu takardu sun iso sa'o'i biyu kafin su shirya tasowa, don taimakawa wajen rage girman jinkiri, wanda yayi sanadiyar wannan matasalar baki daya.

An jinkirtar da sama da jirage dari uku 300 tun daga safiyar Lahadi, a jihar Los Angeles, a filin jirgin saman 'yan sanda sun saka wani hoton mutane a shafin “tweete” wanda yake nuna tsawon layin dubun dubatan mutane da suke jiran a basu tikitin su don tafiya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG