Babu wani abu da bashi da amfani a rayuwar yau da kullun. Wasu matasa a kasar Indonesia, sun kir-kiri wata fasaha ta yin agogon hannu da na bango, da kanana katako da kafintoci ke yarwa.
Sun sama kamfanin su suna “Matoa” A tabakin shugaban kamfanin, su abun da kawai suke bukata shine, idan kafintoci suka dauki babban bangare da suke da bukata, mukuma sai mu tsunto kananan kuma muyi kokarin yankasu gutsul-gutsul, daga nan sai muyi agogo.
A rana sukanyi agogo ashirin da biyar 25, kuma sukan kai wadannan agogunan kasashe kamar tara 9, wadanda suka hada da China, Singapore, Afrika ta kudu, da Amurka. Kudin agogon na kaiwa kamar dallar Amurka saba’in da biyar $75 zuwa dala dari da hamsin $150 kimanin naira dubu talatin da uku 33,000.
Abun tambaya a nan shine, wai matasa sun san da irin wannan dubarun kuwa?