Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaro Dan Shekaru 14 Ya Zama Abun Kwatance A Duniya


Andrew Eggaebraaten
Andrew Eggaebraaten

Cikin dalibai 30 da suka shiga gasar “Broadcom Math” gasar da ake fitar da yara zakaru, da dubban wasu dalibai a fadin kasar Amurka, kan samu babbar lakabi na “Broadcom Masters finalist” a wannan karon wani matashi mai suna “Andrew Eggaebraaten” dan shekaru goma sha hudu 14, shine yazo na biyu a gasar da yasamu kyautar dallar Amurka $10,000 dai-dai da naira milliyan biyu da dubu dari biyu 2,200,000,

Shi dai Andrew, ya kir-kiri wani hannu na “Robo” wanda yake daban da sauran irin wanda ake da su a kasuwanni a duniya, domin kuwa nashi yanayin abubuwa da suka kai hamsin da takwas 58, kuma ana gayama hannun abu da murya yayi. Kana kuma hannun kan iya muttsuke abubuwa ta bangare da ban-da-ban.

Abun ban sha’awa da wannan yaron shine, a shekarun shi goma sha hudu 14, har yazama gwarzo a fannin kere-kere, domin kuwa a zangon karatu na rani da ta wuce, ya koyar da yara masu kanan shekaru yadda ake sarrafa wutar lantarki.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG