Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Singapore Tafi Yara Masu Hazaka A Duniya


brain
brain

Anyi ittifakin cewar kasar “Singapore” itace kasa da ke da yara da sukafi kowa hazaka a duniya wato “Smartest kids” a turance. Hazakar yara na daya da ga cikin abubunwan da yasa kasar tasamu cigaban tattalin arzikin kasa. Kana kuma hanyoyin da su kabi wajen tsara karatun su, ya taimaka matuka wajen cinma wannan nasarar.

Hukumar tantancewa da tsari na ilimin kasa-da-kasa, ta bayyanar da Edinn Na, a matsayin yaro da yafi kowane yaro kaifin basira a fadin duniya. Shi dai yaron, ya samu wannan yabon ne a wasu gwaje-gwaje da aka gudanar a kanshi. Tun yana dan shekaru uku 3, aka bashi wata jarabawa, wanda yaci maki 142, ita dai wannan jarabawar, tana bayyanar da hazakar mutun idan akayimi shi ita. Wanda ya nuna cewar yana da kaifin basira mai yawa.

A tabakin iyayen yaron, sunce shi dai yaron baya da banbanci da sauran yara, illa dai kawai suna kokari wajen bashi duk wasu abubuwa da yake bukata. Kuma a kowace rana kafin yayi bacci, sai sun tabbatar da ya karanta littafi, haka da safe kafin ya tafi makaranta, sai ya karanta littafi da kuma haddace wasu abubuwa. Suna ganin cewar wannan ya taimaka mishi matuka wajen haddace abubuwa, domin kuwa ya zama yaro da bashi da mantuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG