Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dabbobi Na Ganin Abun Da Mutane Basu Gani


Microsft Skype
Microsft Skype

Kyanwa, karnuka, da sauran wasu dabbobi masu shayarwa, suna ganin wasu abubuwa da mutane basu iya gani. Domin kuwa suna iya ganin wani haske da ake kira “Ultraviolet” a turance. Nasu ganin ya ban-banta da irin na mutane, sukan ga wasu abubuwa da idon mutun bazai iya gani ba a wannan duniyar.

A wani bincike da aka gudanar, da yake nuni da cewar, shi dai irin wannan hasken ba wai irin hasken ja da baki bane. Mutane nada wata yana a idamuwan su, wanda yake kare musu damar ganin wannan hasken na “Ultraviolet” amma kuwa su dabbobi suna da kaifin gani ta cikin hasken.

Masana kimiyya sunyi nazari akan ruwan tabarau, na matattun dabbobi masu shayarwa, ciki har da maguna, karnuka, birai, pandas, hedgehogs, da kuma ferrets. Wannan bincike don su gano yawan haske nawa ke wucewa ta cikin ruwan tabarau, da taya yake kai wadannan haske a jiki. Sun kuma ƙarasa da cewa wasu dabbobi masu shayarwa basu iya gani a zahiri sai ta hasken “Ultraviolet”

Babu wanda yake tsammani waɗannan dabbobi zasu iya gani ta ultraviolet, amma a gaskiya suna iya gani. Jagoran wannan binciken ne ya bayyana haka, Mr. Ron Douglas, na sashen binciken halitta a jamia’ar City University a kasar Ingila.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG