Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wake Da Sha'awar Kir-Kiran Mutun-Mutumi Robot?


Almustapha Almustapha
Almustapha Almustapha

Zaben wannan karatun ya biyo bayan korafin rashin jin kamar ina karanta science da nayi a wurin malami na mai bani shawara “Academic adviser” (wadanda makaranta suka ajiye domin luradda yan makaranta da sasu kan hanya ta nasara game da karatu).

A yanzu ina cikin shekarar karshe ta karatun harkar kerekere wato “Engineeing” Yanzu Haka ina cikin “Senior design project” dina. Wanda yazama dole ga duk wanda ya karanta “Electrical and Computer Engineering” sai ya zabi bangare da zai kware a kai. Wanda ni nazabi “Robot” wato mutun mutumi, kasancewar laka’ari da inda fasaha ta kere kere a duniya ta nufata. Nan da Shekara goma sha biyar komi zai koma “robot” yake yin shi.

Don yanzu haka asibitoci na duniya da suka cigaba, da kamfanoni duk da robot suke anfani. Wannan aikin da makaranta ta sakamu tana son mu kera Robot. Manufan kera robot ya zamana mu zamu kera duka bangarorin shi da halayen ayukkanshi. Kamar wutar da zata isheshi aiki da tsarin shigar wutar a cikin jikin shi. Haka kuma jikin shi kamar abubuwanda zai dinga amfani dasu wurin daukar masu bukatar taimako idan yaje wurin hadari. Kuma dole ne Robot din ya kasance zai iya kai kanshi wurinda hadari ya faru. Ya kasance idan ya isa wuwrin zai iya gane wanda yafi jin jiki kuma ya dauke shi zuwa asibiti mafi kusa.

An tanadi filin da za’ayi wannan gasar ne wanda itace kamar jarabawar mu ta karshen karatu da wannan aikin. Wurin yana da hanyoyi na kwarai da masu matsala, kamar wuri mai ruwa, ciyawa, da gini. Kuma yanada asibitoci wurare daban daban.

Daga karshe ina kira ga matasa masu tasowa, da su san cewa sune manyan gobe. Don haka su kara azama wurin neman Ilimi domin shine gishirin zaman duniya. Inda duniya ta nufata idan bakada ilimi to tabbas zaka ka kasance cikin takaici da danasani.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG