McEwen, shine shugaban binciken ta hukumar NASA, ya ce akwai alamun ruwa mai yawa wanda zai iya cika manyan kurmin iyo na filin wasanni da yawa, amma ruwan na kwance ne a wuri mai girma. Masana kimiyya sun ce wannan magudanai na kwance ne a gangare masu wuyar hawa da wuri mai sarkakiya, wanda hakan zai sa yayi wahala ga motocin binciken sararin sama da mutane masu son ganin kwakwaf nan gabasu je can.
McEwen ya ce mutum mutumi zasu iya zuwa kusa, su lura da abubuwa daga nesa. Babbar bukata a nan itace wata rana a kawo wannan ruwa duniyar mu don bincike a kan sa. Green yace tunda yanzu masana kimiyya sun san abun da suke nema, za’a iya gudanar da bincike mafi inganci da tsari.
Mars din yau ba iri daya take sam da Mars din daba. shekaru biliyan 3 da suka wuce da fiye da haka makociyar tamu da tafi kamanceceniya da duniyar mu tana da katon teku, amma wani canji na gabadaya ya faru, wanda ba’a da tabbacin takamaimai me ya faru. Kumbon binciken Mars ya kasance yana zagaye duniyar tun shekara ta 2006.