Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Dabi'u Da Kan Jawo Ma Mutun Raini


Zumunta
Zumunta

Sau da dama mutane kanyi wasu abubuwa da kan ja musu raini, kiyayya, da ma wasu abubuwa makamanta haka. Wani bincike da aka gudanar dake nuni da cewar, akwai wasu abubuwa uku 3, kadan daga cikin abubuwa da sukan sa mutun yayi bakin jini a wajen mutane.

Masu binciken sun bayyanar da cewar, duk mutun da ya kasan ce yana yawan saka hotuna a shafin shi na zumuntar facebook, twitter, kamar a ce mutun yana wani abu sai ya sa hoto, akalla mutun yasaka hotuna masu yawa a rana. Ya zamana dai mutun na yawan saka hotuna, ko yin rubuce-rubuce a shafin na shi wannan na sa mutane suji basu son shi.

Hakama mutun ya kasance yana da yawan abokai a shafin zumunta na yanar gizo kamar facebook, twitter, Instagram, da dai makamantan su, hakan shima yana sa mutane su dinga mai wani kallo. A wannan binciken da aka gudanar dake nuni da cewar idan mutun yana da abokai ma dai-dai ta, to zai zama mai sha'awa kuma ba zai dinga maganganu da basu kamata ba a tsakanin shi da karancin abokan shi.

Duk mutun da ya kasan ce yana yawaita bayyanar da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar shi, wadanda suka kamata mutun yabar ma kan shi ko wasu aminai mafi kusa da shi, to hakan yana jawo mutane su dinga yi mishi kallon banza. Haka shima mutun da ya yawaita cika baki, ko kururuta kai shima mutane basu cika son irin wadannan mutane ba. Ko kuma mutun ya dinga bayyanar da wasu abubuwa dake gudanar tsakanin shi da budurwar shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG