Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniyoyin Wata 3 Zasu Kusanci Juna A Cikin Kwanakin Nan


Duniyar Wata
Duniyar Wata

Masu binciken duniyar wata da taurarin, sun yi hasashen cewar cikin duniyoyi da ake dasu a sararin samaniya, uku daga ciki zasu zo kusa da juna a tsakanin yau Asabar, Lahadi, da litinin. Duniyoyin da zasu kusanci juna sune duniyar “Jupiter” duniyar “Venues” da duniyar “Mars”

Ga duk mai bukatar ganin haka sai ya kalli gabas kamin fitowar rana, a cikin wadannan kwanakin. Duk dai da cewar wadannan duniyoyin suna nesa da juna, da kimanin miliyoyin kilomitoci a tsakanin su, amma mu kuwa zamu gan su kamar suna kusa da juna ne. Ba a cika samun hakan ba duniyoyin su kusanci juna, daga wannan shekarar ana sa ran sai nan da shekarar 2021 ko zasu sake kusantar juna.

Abun da mutane kawai zasu iya lura dasu a lokacin shine, zasu ga taurarin da suke da haske fiye da girman taurari. Girman duniyoyin sunfi na taurari, kuma suna da irin nasu hasken da ya ban-ban ta da yadda ake ganin tauraro.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG