Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Meke Kawo Farinciki Da Annashuwa Bayan Babu Kudi


Murna
Murna

Akan yi mamakin wai menene wasu mutane kanyi, wanda ke sasu farinciki a kowane lokaci? Kowa na son yazama cikin murna da annashuwa! Domin shine abun da babu wanda zaiyi danasanin samun shi. Amma tabbatar da wannan farincikin na wasu tsawon lokutta shine abu mai ban wuya. Rayuwar yau da kullun na cike da wasu matsaloli da kan cirema mutun jin dadin duniya.

Duk dai da hakan akan samu wasu da sukan magance duk wadannan mastalolin a rayuwa. Domin kuwa a kowane lokaci, sukan kasance cikin murna da annashuwa, harma sukan yi maganin zaman duniya da baza suyi danasani ba. Amma abun tambaya a nan shine, menene abun da ya ban-banta wadannan mutane da saura?

Ga wasu kadan daga cikin abubuwan da irin wadannan mutane kanyi wanda yake sasu cikin farinciki a yau da kullun. A cewar Dr. Aiken, idan mutane suna yawaita tafiya da sassarfa ko kuzari, hakan na sa bugun zuciyar su ya kai bugu 10, a cikin minti daya, duk kuma wanda zaiyi hakan na tsawon mintoci 15 zuwa 30, a rana zai kasance cikin farinciki a baki daya ranar.

Ku biyo mu gobe idan Allah, ya kaimu zakuji sauran abubuwa goma 10, da suke sa mutun cikin farinci a kowane lokaci. Koda kuwa bashi da kudi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG