Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Mutuwa Ba Kudin Yima Gawa Hidima! Gara Mutuwar Tsaye


Gawar Fari
Gawar Fari

Al’adar wasu kasashe, da wasu addinai, idan mutun ya mutu akan kashe kudi wajen yima gawar shi hidima, kamin a kaita kabari. A kasar Korea ta kudu, abun bai canza ba, domin kuwa idan mutun ya mutu akan kashe magudan kudi, kuma dubban mutane masoya da abokan arziki kan halarci bukin, wanda ake kwashe kwanaki uku 3, kamin ayi jana’izar shi. Amma sai ga wani abun mamaki ya faru.

Wani mutun mai suna Mr. Song, dan shekaru 47, ya mutu a cikin dakin shi babu wanda yasani, har saida ya fara wari kamin aka gane. Dangin shi basu fito ba don daukar gawar balle har suyi mata jana’iza. Amma sai ga wani fittaccen dan-gwagwarmayar kare hakin bil’adam, mai suna Park Jin-ok, ya dauki dawainiyar yima wannan gawar jana’iza shi kadai.

Mr. Park, dai ya tafi asibitin da aka ajiye wannan gawar, dai-dai bakin firij din da aka ajiye gawar, ya shinfida farin kyalle, ya ajiye kayan marmari, bushashen kifi, da filawa. Duk da sunan karrama gawar, hakan dai ya jawo cecekuce a kasar domin kuwa hakan ya sabama al’adun su. Mr. Park, dai ya kira wannan mutuwar ta Mr. Song ,da cewar itace ake kira “Da karuwa a abinda ake kira mutuwa” don haka al’uma su kara hankali, ba yawan kashe kudi shine gata ba, abun da mutun zai tarasa a can shine gata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG