Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kowane Dan'Adam Da Irin Nashi Bukin Zuciyar!


Shanu
Shanu

Duk dai a cikin irin yadda Allah, keyin mutane daban-daban da halittu daban-daban, wasu kan dauki wasu dabbobi da kan cutar da wasu mutane amma su zasu dauke su, don su koya musu wasu abubuwa da zasu zama abun so da sha’awa gare su dama wasu irin su.

Wani matashi mai suna Su’ mazauni babban birin kasar Taiwan wato Taipei, yana da wani dabba da ake kira “Iguana” a matsayin dabbar shi da yake sha’a don zaman takewa. Shima Mr. Jim Sautner da matarshi, mazauna garin Spruce Grove, a kasar Canada, suna da wani dankareren Shanu da ake kira “Buffalo” shicdai wannan shanu, ba irin sauran shanaye bane, da aka saba dasu, su shanayen Buffalo, an san su da masifa, don haka ake amfani da su wajen wasan nuna gwaninta na hawan shanu da mafadata.

Sai wani yaro mai shekaru goma sha daya 11, yana da wani Kyan-kyaso wato “Cockroach” a turance, ya dauke shi a matsayin abokin wasan shi. Sanin kowane cewar, duk inda aka ga kyan-kyaso guduwa ake, ko dai don irin cuttutuka da zai iya yadawa, ko dan rashin tsaftar shi. Sai gashi wani ya dauka a matsayin abun wasa. Wannan shine ake cema Allah daya gari ban-ban.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG