A kasar Amurka, gwamnati na da hurumin karbar ‘yayan da ka Haifa, musamman idan aka sami iyaye da muzgunama ‘yayan. A jihar Illinois ta kasar Amurka, ana ta takaddama tsakanin wata mata Amanda, da hukumomi, dangane da ‘yayan ta uku 3. A shekarun baya ne aka same ta da saurayin ta sun daure ‘yayan nasu uku, a bayan kujerar mota, suka sasu cikin wani rafi, hardai takai ga yaran suna ihun agaji, amma iyayen basu a wajen balle su basu wani taimako. Hakan yasa aka daukar mata hukuncin kidan kasu.
A shekarar 2003 aka sameta da halin na ko in kula a kan ‘yayanta, wanda saurayinta ya cutar da yaran su uku, taba ma saurayin nata damar muzguna ma yara ne a dalilin cewar yaran suna neman su kawo mata cikasa a soyayyar ta, da saurayin nata. Haka kuma da irin rayuwar lalata da tasa kanta da saurayin nata, kana da shaye-shaye. Wannan saurayin nata shine kuma uban 'yayan.
Alkali ya daukar mata wa’adin shekaru fiyar 5, a gidan kasu, bisa dalilin rashin kula da yaran. Yanzu dai haka ta kare zaman gidan kurkukun, wanda take neman kotu da ta dawo mata da ‘yayan nata. Amma hukumomi na ci gaba da bincike don gano ko ta fahimci dalilin da yasa aka daukar mata wannan hukunci, da kuma yanayin hankalin ta a wannan lokacin.