Amber, itace mahaifiyar wani yaro Leland Shoemake, wanda ya rasu a sanadiyar wata cuta da ta addabi kwakwalwar shi, shi dai yaron dan shekaru shida 6, ya mutu bayan jinya da yayi a asibiti. Tun a lokacin da yake raye, mahaifiyar shi ta lura da wasu abubuwa na daban a yadda yake gudanar da rayuwar shi.
Iyayen shin suna ganin cewar yaron yana da wata baiwa da ta banbanta shi da sauran yara. Yakan yi wasu abubuwa na daban da yadda akasan yara nayi. Bayan mutuwar shi iyayen shi sun koma gida don daukar kayan da za’a sami shi a lokacin birne shi, sai suka ga wata takarda da yabar musu wasiyya.
A cikin wasikar wasiyya da yabar ma iyayen shi da ke nuni da cewar, kamar yasan da cewar zai mutu. Ya rubuta cewar “Har wayau ina tare da ku, ina kara muku godiya Mama da Baba” Ina kara godewa da irin kulawa da kuka bani. Bayan ganin wannan wasikar iyayen yaron sun sake shiga cikin damuwa da rashin yaron. Yanzu haka dai uwar yaron ta kirkiri wani shafin yanar gizo don tunawa da yaron.