Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Daya Gari Banban! Wasu Namun Daji Da Ake Gudu Sune Abun So Ga Wasu


Zaki
Zaki

Saad Eldeen Al-Jamal, wani mutun ne mazauni garin Gaza, yana da ‘yayan zaki guda biyu da ya dauka a matsayin nashi dabbobin da yake sha’awa, a matsayin dabbobin gida. Haka shima Mr. Kheng, dan kasar Thailand, yana da Kada wadda yafison ta da komai a duniya, babu wanda zai iya tunanin cewar Kana na iya zama abun cudanya da mutane, balle har mutun yayi tunanin daukarta a matsayin abun kusanta.

A jihar Florida kuwa ta kasar Amurka, Mr. Steve Sipek, yana da wani koshashen Zaki wanda yake bashi madara a matsayin abun shan shi. Haka wannan zakin shine dabbar da yafi so da komai. Sai mace ta farko Lisa Mcgann, tana da Kunkuru a matsayin abokin rayuwar ta.

A kasar Amurka, abu ne mai wuya mutun yaga Akuya, mutun kan iya gama tsawon rayuwar shi batare ya taba ganin akuya ko wasu dabbobi masu irin wannan nau'in masu rai ba a kasar Amurka. Don haka Mr. Cyrus Fakroddin, ya dauki akuya a matsayin abokiyar rayuwar shi, ya dauke ta watarana suka shiga babban birnin New York wanda ya daukar mata hayar mota don a zagaya da ita ta ga gari.

Ana ku kashashen wadanne dabbobi ne akafi mu'amala dasu? Ku rubutu muna a shafin mu na Dandalinvoa/facebook.com

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG