Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zakarun Waka Masu Aikawa Da Sakonni Na Kasar Amurka


An zabi wasu fitattun mawaka na kasar Amurka, da aka bayyana su a matsayin mawaka da baza’a taba mantawa da su ba a duniya. Dalilin kuwa shine wadannan mawakan sun yi wasu daga cikin wakokin su masu sosa rai, da shiga jiki, haka kuma da bada ma’anoni da yadda rayuwa ke gudana.

Matashin mawakin nan Justin Bieber, shi aka zaba na farko da wakar da yayi mai take “Sorry” wato Hakuri, ita dai wannan wakar yayi tane ga tsohuwar budurwar shi Selena Gome. Sai mawakiya Britney Spears, a wata waka da tayima Justin Timberlake mai take “Cry Me a River” wato Kuka a rafi. Sai Jake Gyllenhaal, da Herry Styles, da John Mayer, Joe Jonas, da Taylor Swoft. Haka da Nick Jonas, sai Miley Cyrus.

An dai yi ittifakin cewar kowannen daga cikin su yayi rawar gani a wajen yin waka mai aikawa da sako masu matukar muhimanci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG