Shahararren mai kudin nan mazaunin babban birinin kasuwanci na kasar China, wato Hong Kong, ya saya ma ‘yar-shi wasu zobuna guda biyu na lu’u lu’u wadanda kudin su ya kai dallar Amurka milliyan saba’in da bakwai $77 wadanda sukayi dai-dai da naira Billiyan gomasha shidda da milliyan dari tara da arba’in 16,940,000,000.
Shidai hamshakin mai kudin Joseph Lau, an tuhume shi da aikata laifin cin hanci da rashawa, anyin bukin saida wadannan lu’u lu’un ne a kasar Geneve, wanda aka kasa su a faifai ga duk wanda ya fi biyan kudi masu yawa, ya dauki zobban. Ita dai wannan yarinyar mai suna Josepine, ‘yar shekaru bakwai da haihuwa ce 7. Bayan sayan wadannan zobunan ya chanzama zobunan suna daga “Blue Moon” zuwa “The Blue Moon of Josephine” wato sunan zobunan guda biyu an kara musu sunan yarinyar tashi a gaba.
Wannan cinikayyar zobunan lu’ lu’u suna daga cikin wadanda aka taba siyar wa da mugun tsada a duniya.