Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe 20 A Duniya Da Yara 'Yan Sakandire Sukafi Kokari


2222221 - Community Activity
2222221 - Community Activity

Babu wani tattalin arzikin kasa da zai iya cigaba idan ba an bunkasa bangaren ilimi a kasar ba. Hakan shine yasa wasu kasashe da dama a fadin duniya sukayima sauran kasashe fintinkau. A wani rahoto da wata hukuma mai suna “Organization for Economic Co-operation and Development” (OECD) suka fitar, na nuni da cewar kimanin kasashe saba’in da shida 76 ne suka shiga cikin wani bincike da aka gudanar.

Wadannan kasashen 76, sune kasashe a duniya da suke da bayanai a rubuce na yadda ake gudanar da tsarin karatu. Cikin wannan alkaluman an iya zakulo kasashe ashirin 20, da suke da yara ‘yan makarantar sakandire da suka fi kowa hazaka a duniya. A wajen tantance wadannan yaran anyi amfani da abubuwa da dama, anyi amfani da yawan maki da suke samu a darasin lissafi, turanci, kimmiya, da kuma yadda yara ke warware matsaloli cikin gaggawa.

Yaran da aka gwada a wadannan makarantun ‘yan shekaru 15 ne. Kasar Ingila itace ta zo ta karshe, inda yara suke samun karatun dole har sai sun kai shekaru 16. Sai kasar Austria, suma yara daga shekaru 15 zuwa 19 ne a matakin sakandire, haka kasar Slovenia, da kasar New Zealand, kana kasar Belgium, da kasar Ireland, harma da kasar Australia, da kasar Germany, kana kasar Vietnam, sai kasar Poland da kasar Canada, haka ma kasar Nertherlands ba a barsu a bayaba, da kasar Switzerland, kana kasar Estonia, kana kasar Finland, da kasar Chinese Taiwan, haka ma kasar Japan, da kasar Korea, sai kasar China, ta farko kuwa itace kasar Singapore.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG