Daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki! Amma hakan na nuna cewar idan aka kalli fuskar mutun, ana iya gane wane irin hali yake ciki. Akan iya gane abubuwa da dama daga kallon fuskar mutun a wasu lokkuta. Babu ma idan mutun amintacce ne ga mutane, haka ma yadda suffar mutun take tana iya bayyanar da lafiyar shi da wasu abubuwa dake damun shi.
A wani bincike da masana kimiyya suka gudanar, akan wasu yanayin fuskoki mutane goma 10, wanda biyar 5, daga ciki suna nuni da wani yanayi na rashin fara'a, yawanci mutane da suka bada tasu fahimtar sun bayyanar da fuskoki masu murmushi a matsayin mutane masu walwala da amintaka a cikin jama’a.
Amma fuskokin da suke babu wani annuri a tare da su, anfi daukar su a matsayin mutane da baza a iya amince ma ba. Sun kara da cewar mafi akasarin ‘yan mata sunfi son ganin fuskar samari masu fara’a da annashuwa, domin a nasu ganin zasu fi samun kwanciyar hankali idan suna tare da na miji da zai damu da irin halin da suke ciki. Amma duk wanda bai da wata annuri a tare da shi, to babu tabbacin zai damu da irin halin da suka samu kansu ciki ba. Wannan yana nuni da cewar a tsakanin maza da mata akai bukatar kowa ya kokarta wajen kyautata mu'ama don kara samun fahimta.