Cikin jerin shugabanin kasar Amurka da sukafi kudi tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1776, kimanin shekaru dari biyu da talatin da tara 239, ke nan da suka wuce. Shugaba “Theodore Roosevelt” shine shugaba da ya zamo na hudu 4, a masu kudi, a dai tarihin shi, ya fuskanci matsalolin rayuwa, duk dai da cewar iyayen shi masu kudi ne, daga jihar New York. Amma ya samu kudin shine ta sanadiyar littattafai da ya rubuta, domin kuwa ya rubuta sama da littafi arba’in 40. A lokacin rayuwar shi ya gina wasu rukunin gidaje masu suna Sagamore Hill Estate. Yana da kudi dallar Amurka $125M dai-dai da naira =N=27,500,000,000
Sai na fiyar 5, a kudi shine “Andrew jackson” shi dai tsohon soja ne, ya samu kudin shi a lokacin da yake aiki, kuma yayi sana’ar saida filaye, a lokacin shine aka wargaza tsarin bankin tarayya. Yana da dallar Amurka $119M dai-dai da naira =N=26,180,000,000
Na shida a kudi kuwa shine “James Madison” wanda akema kirari da "baban kundin tsarin mulki" Ya dai samu kudin shi ne a lokacin da yake ministan cikin gida, da kuma lokacin da yake shugaban kasa. Amma mafi akasarin yawan kudin shi, daga wata katafariyar gona da yake da ita a jihar Verginia, mai suna Montpelier, da aka yanka ta aka sayar. Yana da dallar Amurka $101M dai-dai da naira =N=22,220,000,000