Wasu kasashe a duniya na da karfin tattalin arzikin karkashin kasa, goma daga cikin kasashe na zaune ne a saman arzikin lu’u-lu’u. Kasar India, na da kimanin yawan lu’u-lu’u da yakai 557.7 tons. Kasar itace kasa da tafi kowace kasa a duniya yawan amfani da lu’u-lu’u.
Sai kasar Nerthaland, itama tana da yawan lu’u-lu’u da ya kai 612.5 tons, mafi yawa daga cikin tarin dukiyar su ta lu’u-lu’u, suyar da ita ne ga kasar Amurka. Kasar Japan, a shekarar 1950 tana da adadin yawan lu’u-lu’u 6 tons, amma da suka fara hako danyen lu’u-lu’u, a shekarar 1959, sai da yakai tons 169, zuwa shekarar 2011, kasar ta Japana sun sayar da lu’u-lu’u da ya kai kimanin tiriliyan 20 na kudin kasar wanda ya taimakama arzikin kasar tun bayan girgizar kasa na Tsunami.
Ita kuwa kasar Switzerland, tana da yawan lu’u-lu’u da ya kai 1,040.0 tons a shekarar 2014, mutanen kasar sunyi nuni da rashin yardar su dangane da yadda babban bankin kasar yayi yunkurin kara asusun ajiyar arzikin lu’u-lu’u na kasashen waje. Kasar Russia, nada adadin 1,352.2 tons, kasar dai ita ta zamo kasar da tafi kowacce kasa a duniya sayen lu’u-lu’u a shekarar 2015. Kasar China, kuwa ta zamo kasar da tafi bayyana a matsayin kasa da take sayen lu’u-lu’u a koda yaushe, bayan shekaru 6, da sukayi shuru basu magana akan arzikin su na lu’u-lu’u, sun bayyanar da adadin tarin lu’u-lu’un su da yakai 1,708.5.