Milliyoyin mutane ke ta kokarin murmurewa daga annobar dusar kankara da aka kwashe kwanaki 3 anayi a jihohin yanki Arewa maso gabashin kasar Amurka. A tarhi wannan na daya daga cikin dusar kandakar da aka samu mai dankaran yawa.
Rahotani sun bayyanar da wannan dusar kankarar ta hallaka kimanin mutane 12, wanda 9 daga ciki sun fito daga yankin babban birnin Washignton ne, 5 kuma daga ciki sun fito daga yankin jihar New York. Mafi akasarin su sun samu hadarin motane a yayin da dusar ta fara sauka, wasu kuma sun hadu da cutar bugun zuciya ne a dai-dai lokacin kwasar dusar kankarar don gyaran hanya.
Har ya zuwa ranar Litinin makarantu da ma’aikatu da dama basu koma aiki ba, haka dubban mutane basu samu damar komawa gidajen suba, a sanadiyar rashin tashi da saukar jirage.
Har a jiya babban birnin tarayya Washington DC, ba’ayi ayyuka a ma’aikatu da dama ba, haka jirgin kasa da motocin sufuri babsuyi aiki kamar ko da yaushe ba, sun samar da kiddadagun wuraren zama ga kalilan na mutane da ke kai kawo cikin wasu dalilai masu karfi.
An bayyanar da wannan shine tsabar dusar kankara mai yawa da aka samu tun bayan na watan Fabrairu a shekara 2006, da yakai inci 26.8 na bana yakai 26.9.