Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamshakin Mai-Kudi Ya Taka Shari'a! Shari'a Ta Kuwa Hau Kan Shi


Duk wanda ya taka shari’a to itama zata takashi watan watarana. Haka kuma babu wanda yafi karfin shari’a a inda ake shari’ar gaskiya. Wata kotu a kasar Iran ta yanke ma wani hamshakin mai kudi hukuncin kisa, bisa dalilin samun shi da akayi da laifin cinhanci da rashawa.

An samu hamshakin mai kudin Babak Zanjani, dai da laifi dumu-dumu inda aka tuhume shi dai laifin sace kimanin dallar Amurka billiyan $2.8B dai-dai da naira tiriliyan biyar ke nan. A zamanin tsohon shugaban kasar Mahmoud Ahmadinejad, wanda a wancan lokacin yayi kokarin fitar da kudin daga kasar zuwa wasu kasashe ta hanun bankin daular musulunci na kasar.

Duk dai da cewar zai fuskaci kisa, hakan dai ba zai hana shi biyan dukiyar da ya sace ba, sai ya biya kudin kuma a zartar mishi da hukuncin da kotun ta yanke na kisa. Laifin sata, zanba cikin aminci, da cin hanci da rashawa suna daga cikin manya manya laifufuka akasar. An yanke wannan hukuncin ne a bayyanar jama’a. Wannan hukuncin ya shafi wasu mutane biyu suma wanda yanzu haka su uku zasu fuskanci kisa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG