Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Neman Wani Mutun Da Ya Fado Daga Jirgin Ruwa Hawa Na 10


Royal Caribbean cruise ship Jewel of The Seas
Royal Caribbean cruise ship Jewel of The Seas

Wani mutun mai shekaru 46, da haihuwa Mr. David Mossman, ya fado daga cikin wani jirigin ruwa na ‘yan yawon shakatawa daga hawa na 10. Wannan jirgin na daya daga cikin manya manyan jiragen yawon shakatawa a fadin duniya. Jami’an tsaro na jirgin Royal Caribbean Cruise, na cigaba da bincike cikin karkashin ruwa don gano wannan mutumin.

Ana dai cigaba da neman shi a cikin ruwan inda aka samar da duk wasu kayan agajin gaggawa da zasu taimaka wajen neman shi a cikin ruwan da suka hada da jirgi mai saukar angulu. Mutumin dai ya fada cikin ruwan ne jim kadan bayan tasowar jirgin daga tashar Key Largo, da ke jihar Florida ta nan kasar Amurka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG