Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Habaka Wasan Kwallon Kafar Mata Daga Tushe


‘Yar wasan gaba ta kungiyar kwallon kafa r mata ta Najeriya wato Super Falcons Asisat Oshoala ta bukaci da a kara kaimi a wajen habaka wasan kwallon kafa na mata a duniya daga tushe masamman ma a nahiyar Afirka.

Ta furta haka ne a wani taron hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA akan kwallon mata da shugabanci da aka gudanar a kasar Switzerland wanda aka yiwa taken adalci wajen kaddamar da sauye sauye.

Asisat ta kuma yi kira ga shuwagabanin FIFA a Afirka da masu kula da wasan kwallon kafa da kuma wadanda suka yi fice a faggen wasan kwallon kafa dasu taimaka wajen ciyar da wasan kwallon mata gaba.

Tace a nahiyar Afirka masamman ma a Najeriya akwai wasu bangarori da suke ganin cewa wasan kwallon kafa bana mata bane domin suna ganin cewa zai wahalar dasu .

Ta kara da cewa babu kyawawan wuraren buga wasan kwallon kafa saboda zaka ga ana wasan kwallo akan burji ko kuma yashi.

XS
SM
MD
LG