Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanyoyin Kaucema Kamuwa Da Cutar Kansa


Cutar kansa da akafi sani da cutar daji, na daya daga cututtuka da kan kashe mutane tun da kuruciyar su, yawancin mutane da ke mutuwa a fadin duniya a wannan zamanin su kan kamu da cutar kansa. Wasu masana sun gudanar da wani bincike, wanda suka iya gano wasu abubuwa da dama da suke haifar da cutar kansa.

Kuma sun bayyanar da nau’oin kansa daban-daban, wanda suke ganin idan mutane zasu gaggauta magance cutar tun tana sabuwa, to babu shakka za su iya rabuwa da cutar har’abada. A cikin jerin alamomin kamuwa da cutar kansa, sun hada da yadda mutun zai dinga jin jikin shi yana yawan mutuwa da jin kasala akai-akai.

Haka kuma idan mutun yana ramewa batare da wani dalili ba, shima akwai bukatar mutun ya binciki hakan, domin kashi 60% na mutane da ke ramewa, ko dai ya zama mutun na fama da kansar cikin ciki ko kuma na hanta. Haka ma idan mutun yana yawan samun kunburin ciki batare da wani dalili ba, shima yana iya zama mutun na dauke da cutar kansa, haka yawan ciwon kai na iya zama hanyar kamuwa da cutar ta kansa. Idan mutun na samun matsalar karancin nunfashi, to shima ya garzaya asibiti don ganin likita a kan lokaci. Idan mutun ya fara ganin wani canji a fatar jikin shi to shima ya kan iya zama daya daga cikin jerin alamu na cutar kansa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG