Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pharoahs Ta Shirya Tunkarar Super Eagles


Gabani karawar da za’a yi tsakanin Kungiyar Super Eagles ta Najeriya da Pharoahs ta kasar Masar, mai horas da ‘yan wasan na Masar, Hector Cuper, tuni ya bayyana sunayen ‘yan wasan da zasu taka leda a karawarsu da Super Eagles.

Koda yake har yanzu Samson Siasia, bay bayyana sunayen ‘yan wasan da zasu buga wasa a karawar da Najeriya, zata yi da kasar Masar ba, daga dukkan alamu Samson Siasia ya sha damarar samun nasara.

Kasar Masar wace ta kasance ta lashe kofin na nahiyar Afirka har sau uku a jere a shekarun 2006, 2008 da 2010 zata fafata da Najeriya a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna, a ranar 25, ga wannan wata na Maris da muke ciki,

Daga bisani bayan kwanaki hudu Najeriya zata ziyarci kasar Masar domin buga wasa zagaye na biyu.

A farkon makon nan ne Hector Cuper ya gayyato wasu ‘yan kasar dake wasa a kasar waje domin takawa kasar Masar leda a karawarta da Najeriya.

XS
SM
MD
LG