Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutun 2 Sun Mutu Da Dama Sun Jikkata Bayan Wasan Kwallon Kafa A Morocco


Morocco Soccer Club World Cup
Morocco Soccer Club World Cup

A ranar Asabar da ta gabata ne akayi dauki ba dadi tsakanin magoya bayan ‘yan wasan kwallon kafar Raja Casablanca da ‘yan kungiyar Chabab Rif Al Hoceima, na kasar Morocco. Rikici ya kacame a tsakanin magoya bayan kulob din biyu, bayan tashi da akayi a wasa da ci 2 da 1, inda kungiyar Raja Casablanca su kayi nasara.

A lokacin rikicin dai mutun biyu sun rasa ran su, haka kuma sama da mutane 49, sun samu munanan raunuka. Ita dai kungiyar ta Raja, tana daya daga cikin kungiyoyin kwalon kafa mai girma a kasashen yankin Afrika ta gabas.

Dama dai ‘yan kungiyar ta Raja, da magoya bayan su, an taba saka musu takunkumi, don gujema irin rikici makamanci hakan. A yanzu dai haka an sakama kungiyar tara na kimanin naira milliyan 23,000,000 kuma bazasu samu damar buga wasanni biyar ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG